Mario Balotelli ba zai bar Liverpool ba

Mario Balotelli Hakkin mallakar hoto PA
Image caption An yi rade -radin cewar Liverpool ba za ta ci gaba da zama da Mario Balotelli ba

Mario Balotelli ba zai bar kungiyar Liverpool ba a karshen kakar wasan bana in ji eja dinsa Mino Raiola.

Balotelli ya koma Liverpool daga AC Milan kan kudi £16m a watan Agustan 2014, sai dai kuma kwallo daya ya ci a gasar Premier tun komawarsa Anfield wasa.

A wata hira da aka aka tambayi Raiola ko Balotelli zai bar Liverpool a wata kafar watsa labarai, ya ce sun tattauna da Liverpool kuma dan wasan zai ci gaba da zama a Anfield.

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya fada a watan Janairu cewar ya kamata Balotelli ya kara kai mi ya kuma gane salon tamaular da suke buga wa.

Liverpool ta kammala gasar Premier bana a mataki na shiga da maki 62 daga wasanni 38 da ta buga.