Senegal ba ta gayyato Cisse da N'Doye ba

Papiss Cisse
Image caption Dan wasan ya samu matsala a gasar Premier kan tofa yawu tsakaninsa da Evans na Man United

Senegal ba ta gayyato Papiss Cisse na Newcastle da Dame N'Doye na Hull City cikin tawagar kwallon kafarta ba.

Senegal din za ta karbi bakuncin Burundi a wasan neman gurbin shiga Gasar cin Kofin Nahiyar Afirka na shekarar 2017.

Rabon da Cisse mai shekaru 29, ya buga wa Senegal tamaula tun lokacin da kasar ta dauko sabon koci Alio Cisse a watan Maris.

Haka su ma Mousa Sow da gola Bouna Coundoul da Papa Kouli Diop da Diafra Sakho ba a gayyace su.

Sai dai Senegal ta kira Demba Ba cikin tawagar, gannin yadda dan wasan mai shekaru 30 ya ci kwallaye 18 a gasar Turkiya da Besiktas a bana.

Senegal tana rukuni na 10 da ya kunshi Burundi da Niger da kuma Namibia.