"Benteke yana da farashi idan zai bar Villa"

Christian Benteke Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya yi fama da jinyar rauni a farkon kakar wasan bana

Kocin Aston Villa Tim Sherwood ya ce abu ne mai wuya mu hana Christian Benteke zuwa duk kungiyar da ta yi zawarcin daukarsa.

Sherwood ya fada cewar dan wasan yana da farashi da aka kayyade idan zai bar Villa a lokacin da ya rattaba kwantiragi.

Benteke wanda ya ci wa Villa kwallaye 15 a kakar wasannin bana, ana rade-radin zai koma taka leda a kungiyar Liverpool a badi.

Sherwood ya ce ba zai fayyace kudin da aka kayyade idan wata kungiya na son daukar dan wasan ba, amma rahotanni na cewar kudin ya kai £32.5m.

Benteke ya koma murza leda a Villa daga kulob din Genk kan kudi £7m a shekarar 2012. A inda ya rattaba kwantiragin shekaru hudu.