Benitez ya tabbatar da zai bar Napoli

Rafael Benitez
Image caption Benitez ya horar da Chelsea kafin ya koma Napoli ta Italiya

Rafeal Benitez ya ce zai bar aikin horar da Napoli da zarar an kammala gasar Serie A ta Italiya a ranar Lahadi.

Ana rade-radin cewar zai koma Real Madrid ne domin ya jagorance ta, wacce ta kori kociyanta Carlo Ancelotti ranar Litinin.

Kungiyar Napoli tana mataki na hudu a teburin Serie A, kuma za ta buga wasan karshe da Lazio a kokarin da take yi na neman gurbin shiga gasar cin kofin Zakarun Turai na badi.

Benitez ya ki ya amince ya sabunta kwantiraginsa da Napoli, domin ya koma Madrid wacce ya horar da matasan kungiyar 'yan kasa da shekaru 19 a shekarar 1990.

Idan Benitez ya koma horar da Madrid, zai zamo karo na biyu da zai koma kasarsa Spaniya tun lokacin da ya bar Valencia domin jagorantar Liverpool a shekarar 2004.

Kocin ya lashe kofin La Liga da na Uefa da Valencia, yayin da ya jagoranci Liverpool ta lashe kofin zakarun Turai a shekarar 2005.