Blatter ya ki sauka daga shugabancin Fifa

Sepp Blatter Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Blatter yana son a sake zabarsa karo na uku kan shugabancin Fifa

Sepp Blatter ya ki ya yi murabus daga jagorantar Fifa, bayan da shugaban hukumar kwallon kafar Turai Michel Platini ya bukace shi da ya yi.

Blatter yana neman a zabe shi karo na biyar a matsayin shugaban Fifa, yayin da zai yi takara tare da Yerima Ali Bin Al Hussein na Jordan a ranar Juma'a.

Blatter mai shekaru 79, ya yi taro da manyan jami'an Fifa a ranar Alhamis, bayan da hukumar ta sake shiga rikita-rikitar cin hanci da rashawa da aka zarge ta da yi.

Bayan nan ne kuma Blatter ya gana tsakaninsa da shugaban hukumar kwallon kafar Turai Michel Platini, wanda ya bukaci da ya yi murabus daga kan mukaminsa.

Wasu daga cikin masu fada a ji a harkar kwallon kafa sun yi kiran da a jinkirta yin zaben, bayan da jami'an tsaro suka tsare mambobin Fifa a Zurich ranar Laraba.