Arsenal ta dauki kofin FA karo na 12

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Arsenal ta dauki kofin kalubale karo na 12

Arsenal ta lashe kofin kalubalen bana, bayan da ta doke Aston Villa da ci 4-0 a karawar da suka yi a Wembley ranar Asabar.

Arsenal wacce ke rike da kofin bara ta ci kwallayenta hudu ne ta hannun Walcott da Sanchez da Mertesacker da kuma Giroud.

Da wannan nasarar Arsenal ta kafa tarihin wacce ta fi daukar FA, bayan da ta lashe kofi na 12 jumulla.

Haka kuma kocin Arsenal Arsene Wenger ya yi kan-kan-kan da tsohon kociyan Aston Villa George Ramsey wajen yawan lashe FA, yayin da da kowannen su ya dauki sau shida.

Lashe kofin FA da Arsenal ta yi ya sa ana ganin ta kammala kakar wasannin bana cikin nasara, bayan da ta kare a mataki na uku kan teburin Premier.

Aston Vila wacce take da tarihin daukar kofin FA karo shida a baya ta kammala gasar Premier bana ne a matsayi na 17 da maki 38.