PSG ta dauki kofuna 3 a bana a Faransa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan wasan PSG suna murna

Paris St-Germain ta kafa tarihin kungiyar da ta dauki kofuna uku a kakar wasa daya a Faransa.

PSG ta kammala daukar kofinta na uku a bana ne bayan da ta doke Auxerre da ci daya mai ban haushi a kofin kalubale ranar Asabar.

Kuma wannan shi ne karo na biyar da ta dauki kofin jumulla, wanda kuma ta lashe Ligue 1 na Faransa shi ma karo na biyar a tarihi a bana.

Tun lokacin da za a fara bude gasar kakar bana ta Faransa PSG ta dauki trophes des Champions, shi kuma karo na hudu da ta lashe a tarihi.

Kociyan PSG Laurent Blanc y ace "Sun kammala kakar wasannin bana cikin nasara, kuma sun yi kishirwar lashe wannan kofin ga shi kuma sun kai ga ci".