Za mu lashe kofin Premier a badi — Walcott

Theo Walcott Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsene Wenger ya dauki kofin FA karo na shida a tarihi

Dan kwallon Arsenal Theo Walcott ya ce ya kamata su kalubalanci lashe kofin Premier badi, tbayan da suka dauki kofin FA na 12 jumulla a ranar Asabar.

Arsenal ta doke Aston Villa ne a wasan karshe da ci 4-0 a Wembley, kuma Walcott ne ya fara ci wa Arsenal kwallon farko.

Sai dai kuma Arsenal ta kammala gasar Premier bana a mataki na uku, wacce rabon ta da daukar kofin tun a shekarar 2003-04.

"Kofin Premier badi shi ne abin da za su yi kokarin su dauka da zarar an fara kakar wasannin shekara mai zuwa," in ji Walcott.

Walcott ya yi fama da jinyar raunin da ya ji a gwiwarsa a Janairun 2014, wanda hakan ya hana shi buga wasan karshe a kofin FA da Arsenal ta doke Hull City 3-2 a Wembley.