An doke Napoli a wasan karshen Benitez

Napoli Lazio Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Napoli ta kammala gasar Serie A da maki 63 a mataki na biyar a kan teburi

Wasan karshe da Rafeal Benitez ya yi da Napoli ya sha kashi a hannun Lazio da ci 4-2, a wasan rufe gasar Serie A Italiya da suka yi a ranar Lahadi.

Tun farko Lazio ce ta fara zura kwallaye biyu ta hannun Parolo da Candreva, bayan da aka dawo daga hutu ne Higuin ya farkewa Napoli kwallaye biyun da aka zura mata a raga.

Sai dai kuma Lazio ta yunkuro a karo na biyu a inda ta kara kwallaye biyu a ragar Napoli ta hannun Onazi da kuma Klose.

Da wannan sakamakon Napoli ba ta samu gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai na badi ba, domin ta kare a mataki na biyar a teburin Serie A bana.

Ita kuwa Lazio ta kammala gasar bana a teburin Seria A a matsayi na da maki 69, biye da Roma wacce take mataki na biyu a teburin da tazarar maki daya kacal.

Ana sa ran Benitez wanda ya taba horar da kungiyar Madrid ta biyu zai karbi ragamar jagorantar Babbar kungiyar Real Madrid.