Afirka ta Kudu ta bai wa jami'an Fifa $10m

South Afirka Fans Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An zargi wasu manyan jami'an Fifa da cin hanci da rashawa

Wata kafar yada labarai a Afirka ta Kudu ta ce kasar ta biya $10m ga jami'an Fifa karkashin Jack Warner wanda ake zargi da cin hanci da rashawa.

Kafar yada labaran ta ce shugaban kwallon Afirka ta Kudu Danny Jordan ya tabbatar da cewar daga kudin da Fifa ta bai wa kasar a shekarar 2008 aka fitar da kudin.

Daga nan ne kuma aka aike wa da hukumar kwallon kafar Afirka ta Kudu da wata wasika wacce ta umarci a aika da kudin zuwa kungiyar kwallon kafar Caribbean.

Jami'an Afirka ta Kudu sun ce kudin ba cin hanci bane domin a ba su daukar nauyin bakuncin gasar kofin duniya a shekarar 2010.

Sai dai kuma masu shigar da kara a Amurka sun ce Afirka ta Kudu ta biya kudaden da ba su dace ba, bayan da gwamnatin ta yi wa Jack Warner tayin $10m domin a bata bakuncin kofin duniya.

Fifa ta amince ta bai wa Afirka ta Kudu bakuncin gasar cin kofin duniya maimakon Morocco wacce suka yi takara a tare.