Damben Gargajiya a Dakwa Abuja

Mai Caji Sunusi dan Gusau
Image caption Mai Caji daga Kudu da Sunusi dan Gusau daga Arewa babu kisa a wannan damben da suka taka

Ranar Litinin ce za a rufe gasar damben gargajiya da ake yi a gidan damben Ali Zuma dake Dakwa a Abuja Nigeria.

Sarkin Dakwa Dr Alasan Musa ne ya saka kambu da ladan naira 300,000 da za a rabawa 'yan damben da suka yi fice a gasar.

Damben dai ana yi ne tsakanin Kudu da Arewa a inda kowannen su ya fitar da 'yan dambe biyar da suke wakiltarsu.

'Yan damben dake wakiltar Kudu sun hada da Shagon Babangida Kurde da Garkuwan Mai Caji da Shagon Bahagon Bala da Shagon Kwarkwada da kuma Bahagon Sani Mai Caji.

'Yan Daben Arewa kuwa sun hada ne da Shagon Bahagon Musa da Bahagon Alin Tarara da Audu dan Kirisfo da Dogo dan Bunza da kuma Sojan Kailu.

Tun a ranar Talatar da ta gabata aka fara gasar, yayin da bangaren Kudu ke kan gaba, bayan da ya yi nasara da kisa 4-2.

Duk wanda ya yi na daya a gasar zai lashe kudi naira 150,000 da kuma kambun dambe, sannan kuma a bai wa na biyu naira 100,000 da kuma sauran kyaututtuka da za a bayar.