Klopp zai huta da tamaula shekara daya

Jurgen Klopp
Image caption Ana rade-radin Jurgen Klopp zai koma horar da tamaula a Ingila da Liverpool

Jurgen Klopp ya ce zai yi hutu daga shiga harkokin wasan kwallon kafa na shekara daya, bayan da ya ajiye aikin horar da Borussia Dortmund.

An yi ta rade-radin cewar kocin zai koma horar da Liverpool ne tun lokacin da ya sanar da cewar zai yi ritaya a karshen kakar bana.

Klopp ya yi rashin nasara a wasan karshe da ya yi, a inda Wolfsburg ta doke Dortmund da ci 3-1 a gasar kofin FA na Jamus ranar Asabar.

Kociyan ya lashe kofunan Bundesliga biyu da kofin FA, sannan ya kai Dortmund wasan karshe a gasar kofin zakarun Turai a shekarar 2013.

Dortmund ta ce tsohon kociyan Mainz Thomas Tuchel ne zai maye gurbin Klopp a kungiyar.