Uefa: Watakila United ta kara da Monaco

Manchester United Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bara a mataki na 7 United ta kammala kan teburin Premier

Watakila Manchester United za ta iya haduwa da Monaco a wasan neman cike gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai ta badi.

A bana dai United ta kammala gasar Premier ne a mataki na hudu, dalilin da ya sa kenan za ta yi wasan cike gurbin shiga gasar.

Monaco wacce ta fitar da Arsenal a gasar bana a wasannin kungiyoyi 16 da suka rage a gasar ta kuma yi rashin nasara a hannun Juventus a wasan zagayen gaba.

Haka kuma za a iya hada United wasa da kungiyar Lazio ko kuma Sporting Lisbon.

Sauran kungiyoyin da za su buga wasannin cike kurbin shiga gasar sun hada da Anderlecht da CSKA Moscow da Fenerbahce da Panathinaikos da Sparta Prague da kuma Young Boys.

Rabon da United ta buga wasan cike gurbin shiga gasar kofin zakarun Turai tun shekaru 10 da suka wuce, bayan da ta doke kungiyar Debrecen ta Hungary.