Ya kamata a girmama Afirka - Nyantakyi

Kwesi Nyantakyi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kwesi Nyantakyi ya ce Afirka tana da 'yancin zabar abin da taga ya dace da ita

Shugaban hukumar kwallon kafar Ghana Kwesi Nyantakyi ya bukaci mambobin hukumar kwallon kafa ta Fifa da su kara girmama Afirka.

Ya yi wannan kiran ne a lokacin da ake sukar Afirka da kada kuri'un da suka sa Sepp Blatter ya kara cin zaben shugabantar Fifa karo na biyar a ranar Juma'a.

Nyantaki ya ce "Abin takaici ne a tambaye ni dalilan da ya sa na zabi Blatter, kuma wadanne dalilan ne da za su sa ba zan zabe shi ba".

Shugaban kwallon kafar Ghana ya ci gaba da cewar mai ya sa ba'a hangen cewar suna da 'yancin bayyana ra'ayinsu da kuma tunaninsu na kansu ba.

Nyantakyi ya yi wadan nan kalaman ne a lokacin da aka damke wasu jami'an Fifa da ake zargi da cin hanci da rashawa.