Chiellini zai gaisa da Suarez a kofin Turai

Chiellini Suarez Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Barcelona da Juventus dukkansu na fatan lashe kofi na uku a kakar wasan bana

Dan kwallon Juventus Giorgio Chiellini ya ce zai yi hannu da Luis Suarez idan suka hadu a karon farko tun bayan da Suarez ya cije shi a gasar kofin duniya a Brazil.

Dalilin cizon da Suarez ya yi wa Chiellini a karawar da aka yi tsakanin Uruguay da Italiya ce ya sa aka yanke masa hukuncin hana shi shiga sabgogin wasanni har tsawon watanni hudu.

'Yan wasan biyu za su sake haduwa a wasan karshe na Gasar cin Kofin Zakarun Turai ranar Asabar a Berlin.

Abokin wasan Chiellini Patrice Evra ya ki yin hannu da Suarez saboda kalamun wariya da yake zargin Suarez ya yi masa a lokacin da aka kara tsakanin Liverpool da Manchester United.

Barcelona wacce ta lashe kofin La Liga da Copa del Rey za ta kara da Juventus wacce ta dauki kofin Serie A da kuma kofin kalubalen Italiya.