Jamus ba za ta kauracewa kofin duniya ba

Wolfgang Niersbach Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana zargin wasu jami'an Fifa da cin hanci da rashawa

Hukumar kwallon kafar Jamus ba za ta goyi bayan kauracewa Gasar cin Kofin Duniya ta 2018 ba, domin nuna bacin rai kan yadda ake tafiyar da lamuran Fifa.

Shugaban hukumar kwallon kafar Ingila Grek Dyke ya ce za su marawa duk wani yunkurin hukumar kwallon kafar Turai kan adawa da sake zabar Sepp Blatter a karo na biyar.

Sai dai a lokacin da yake jawabi a taron hukumar kwallon kafar Turai shugaban hukumar kwallon kafar Jamus Wolfgang Niersbach ya ce ba sa bukatar bin hanyar kauracewa gasar ba.

An zabi Blatter mai shekaru 79 ya ci gaba da jagorancin Fifa duk da danke wasu jami'an hukumar da ake zargi da cin hanci da rashawa.