Ancelotti ya juya wa AC Milan baya

Hakkin mallakar hoto z
Image caption Ancelotti ya taba jagorantar Chelsea

Carlo Ancelotti ya ki amincewa ya kara komawa AC Milan a matsayin kocin tawagar 'yan kwallon kulob.

A makon da ya gabata ne, Real Madrid ta sallami Ancelotti mai shekaru 55.

Ancelotti ya tattauna da shugaban Milan, Adriani Galliani a kan batun ya kara koma wa jan ragamar kungiyar, wacce a baya ya lashe gasar zakarun Turai tare da ita har sau biyu.

Milan ta kamalla kakar wasan da ta wuce a matsayin na 10 a kan tebur a karkashin jagorancin Filippo Inzaghi.

Ancelotti ya ce "Ina godiya ga AC Milan da ta nuna sha'awa a kai na. Amma ina bukatar hutu kuma ina yi wa kungiyar fatan alheri."