Rodgers zai ci gaba da horar da Liverpool

Hakkin mallakar hoto All Sport
Image caption Liverpool ta kammala Premier bana a mataki na 6 bisa teburi

Brendan Rodgers zai ci gaba da jagorantar Liverpool a badi, bayan da ya gana da daya daga cikin shugabanta Tom Werner.

Werner mai shekaru 42 ya tattauna da Rodgers a inda suka yi bitar rawar da Liverpool ta taka a kakar wasannin bana.

Liverpool ta kammala gasar Premier bana ce a matsayi na shida a kan teburi, sannan ba ta samu gurbin shiga Gasar cin Kofin Zakarun Turai ta badi ba.

Werner da Rodgers sun cimma matsaya domin tabbatar da kungiyar ta samu ci gaba a kakar wasannin da za ta yi a badi.

Liverpool ta dauki Rodgers ranar 1 ga watan Yunin 2012, kuma a wasan karshen Premier bana ya ce yana fuskantar kalubale a aikinsa.