Mun karbi cin hanci a Fifa - Blazer

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tsohon jami'in Fifa Chuck Blazer

Tsohon jami'in Fifa Chuck Blazer, ya fayyace yadda suka dinga karbar cin hanci da rashawa tun daga shekarar 2013 a lokacin sauraren kara a New York.

Ya ce shi da wasu kwamitin amintattun Fifa sun amince su karbi cin hanci da ya jibanci zabar Afirka ta Kudu da ta karbi bakuncin kofin duniya a shekarar 2010.

Blazer dan Amurka, ya kuma ce ya karbi cin hanci a bikin gasar kofin duniya na shekarar 1998.

Amurka ce take gudanar da bincike kan zargin cin hanci da rashawa da ya mamaye Fifa wanda har ya jawo shugaba Sepp Blatter ya ce zai yi Murabus.

Masu shigar da kara a Amurka ne suka maka jami'an Fifa su 14 kotu, kan zargin cin hanci da cuku-cuku da halasta kudaden haram.

Sashin hukumar shari'ar Amurka ya zarge su da karbar cin hanci da yankan baya da aka kiyasta ta kai ta sama da dala miliyan 150 a tsakanin shekaru 24.