An tuhumi Wilshere da rashin da'a

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal ce ta doke Aston Villa a wasan karshe a kofin FA a Wembley

Hukumar kwallon kafar Ingila ta tuhumi dan wasan Arsenal Jack Wilshere da nuna rashin da'a a lokacin da suke shawagin murnar lashe kofin FA ranar Lahadi.

Dan wasan mai shekaru 23 ya jagoranci magoya bayan Arsenal wajen yin wakokin muzanta abokan hamayyarsu Tottenham, daga baya ya nemi afuwa.

Hukumar FA ta ba shi daga nan zuwa ranar 10 ga watan Yuni domin ya kare kansa bisa zargin da take yi masa.

An taba tuhumarsa da aikata irin wannan laifin a bara, lokacin da suke yin murnar daukar kofin FA a lokacin.