Afirka ta Kudu ta musanta bayar da cin hanci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fifa ta shiga badakalar zargin cin hanci da rashawa da ake zargin wasu jami'anta

Kasar Afirka ta kudu ta sake musanta zargin cewa ta ba da cin hanci wajen karbar bakuncin garsa cin kofin duniya da aka yi a kasar a shekara ta 2010.

Ministan wasannin kasar Fikile Mbalula ya ce kasarsa za ta hada kai da Amurkawan da ke bincike, amma ba ta da hannu a dambarwar da Amurka ke yi da wasu jami'an Hukumar FIFA.

Ya ce ya rage ga Birtaniya da Amurka su ji da yakin da ke gabansu, kuma sun yi nasarar ganin bayan mulkin mallaka ba za su saurara wa irin wannan mulkin ta bayan-gida ba.

Mr Mbalula Ya ce dala miliyon goma da ake magana, Afirka ta kudu ta ba da su ne a matsayin gudummuwa don habaka kwallon kafa a tsakanin al'umar Afirka da ke yankin Caribbean, kuma sai bayan wasu shekaru da karbar bakuncin gasar, sannan Afirka ta kudu ta ba da kudin.