AC Milan na daf da sallamar Inzaghi

Image caption Ancelotti ya ki amincewa ya koma horar da AC Milna

Kulob din AC Milan na Italiya na daf da raba gari da kociyansa Filippo Inzaghi a cikin makonnan, kasa da shekara daya da kama aikin.

Kulob din dake murza leda a gasar Serie A ya shaida wa BBC cewar Inzaghi mai shekaru 41, ba zai ci gaba da kocin Mila a badi ba.

Milan ta kammala gasar Serie A bana a mataki na 10 a kan teburi, kuma ta gaza samun gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai ta Badi.

Carlo Ancelotti ya ki amincewa ya koma horar da Milan a tayin da ta yi masa, ana hasashen tsohon kocin Sampdoria Sinisa Mihajlovic ne zai maye gurbin Inzaghi a Milan din.