Fifa ta bai wa Ireland toshiyar baki

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Blatter ya ce zai sauka daga shugabancin Fifa bisa zargin cin hanci da rashawa

Kasar Ireland ta ce hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta ba ta toshiyar baki, bisa matakin shari'a da ta so ta dauka kan Thierry Henry.

Ireland ta yi kokarin daukar matakan shari'a kan kwallon da Henry ya zura mata a raga da hannu a lokacin da suka kara a wasan cike gurbin shiga gasar cin kofin duniya a shekarar 2009.

Shugaban hukumar kwallon kafar Ireland John Delaney ya ce hukumarsa tana da shaidun da za ta nuna kan Fifa din.

Delaney ya ce sun cimma yarjejeniyar karbar toshiyar baki, bayan da Ireland ta kasa samun gurbin shiga gasar kofin duniya a Afirka ta Kudu.

An ce kudin da Fifa ta bai wa Ireland sun kai yuro miliyan biyar.