Everton ta dauko Tom Cleverly

Hakkin mallakar hoto ge
Image caption Kwantiragin Cleverly zai kare a United ranar 1 ga watan Yulin bana

Dan kwallon Manchester United Tom Cleverly ya kulla yarjejeniyar kwantiragin shekaru biyar da kungiyar Everton.

Dan wasan mai shekaru 25, wanda ya buga wa Aston Villa wasanni aro a bana, zai koma Everton ne ranar 1 ga watan Yuli, yayin da kwantiraginsa zai kare da United a lokacin.

Haka kuma tawagar kwallon kafar Ingila ta gayyace shi wasan sada zumunta da za ta yi da Jamhuriyar Ireland ranar Lahadi, domin maye gurbin Ryan Mason wanda ya ji rauni.

Cleverly wanda ya buga wa Ingila wasanni 13 a baya, ya kuma yi wasa aro a kungiyar Leicester da Watford da kuma Wigan.