Ina da kwarin gwiwa kan Sterling —Rodgers

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ingila tana da maki 15 a mataki ta daya a teburi a rukuni na biyar

Kocin Ingila Roy Hodgson ya ce matsin da Raheem Sterling saboda yana so ya bar Liverpool ne yake shafar kwazonsa a tawagar kwallon kafar kasar.

Sterling na shan suka sakamakon shirin da yake yi na barin Liverpool, yayin da ya ki amincewa da fan 100,000 da kungiyar ta yi tayin ba duk mako.

Dan kwallon mai shekaru 20 ya kasa taka rawar gani a wasan sada zumunta da Ingila ta tashi wasa babu ci da Jamhuriyar Ireland ranar Lahadi.

Hodgson ya ce "Sterling yana cikin yanayin tsaka mai wuya, amma har yanzu ina da kwarin gwiwa a kan dan wasan".

Wasu magoya bayan Ingila sun yi ta yi wa Sterling kuwwa a Dublin har zuwa lokacin da aka sauya shi a wasan a minti na 65.

Ingila za ta kara da Slovenia a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai a mako mai zuwa.