Fifa: Watakila a karbe tikitin Rasha da Qatar

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ana zargin wasu jami'an Fifa da cin hanci da rashawa

Rasha da Qatar za su iya rasa tikitin karbar bakuncin gasar kofin duniya, idan har aka samu shaidun cewar sun bayar da cin hanci ga jami'an Fifa.

Wannan jawabin ya fito ne daga bakin shugaban kwamitin bincike da kuma tabbatar da bin ka'idojin kashe kudade na hukumar kwallon kafa ta duniya, wato Fifa.

Ya kara da cewa za a iya soke damar karbar bakuncin gasar kofin duniya da aka bai wa kasashen da zarar an samu shaidar cewa saboda sun bayar da cin hanci ne aka ba su takarar.

Rasha aka bai wa izinin karbar bakuncin Gasar cin kofin duniya ta 2018, yayin da Qatar za ta karbi bakuncin wasannin 2022.

A makon jiya ne aka yi awon gaba da jami'an Fifa a Zurich a lokacin babban taron hukumar, bisa zargin cin hanci da rashawa.

An sake zabar Sepp Blatter wanda ya fara jagorantar Fifa a shekarar 1998, ya ci gaba da shugabanci, amma kwanaki hudu tsakani ya ce zai yi murabus saboda badakalar da ta mamaye hukumar.