Barcelona ta dauki Aleix Vidal

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Barcelona ta lashe kofuna uku a bana tare da koci Luis Enrique

Kungiyar Barcelona ta kulla yarjejeniyar daukar dan wasan Sevilla mai tsaron baya Aleix Vidal kan kudi fam miliyan 16, duk da hana ta musayar 'yan kwallo da Fifa ta yi.

Fifa ta dakatar da Barca daga sayo 'yan wasa a shekarar 2015, bisa samunta da aka yi da karya ka'idar daukar matasa 'yan kasa da shekaru 18 ta dokar hukumar.

Vidal mai shekaru 25, ya rattaba kwantiragin shekaru biyar, amma ba zai buga wa Barca tamaula ba har sai watan Janairun 2016.

Barcelona ta dauki dan kwallon ne domin maye gurbin Dani Alves wanda kwantiraginsa zai kare da kungiyar.

Barcelona ta lashe kofin La Liga da Copa del Rey da kuma kofin zakarun Turai wanda ta lashe a ranar Asabar bayan da ta doke Juventus.