Liverpool ta dauko Danny Ings

Hakkin mallakar hoto empics
Image caption Liverpool ta kammala gasar Premier bana ne a mataki na 6 kan teburi

Kulob din Liverpool ya sanar da dauko dan wasan Burnley mai zura kwallo a raga Danny Ings.

Dan kwallon zai koma taka leda a Anfield ne ranar 1 ga watan Yuli a lokacin da kwantiraginsa a Turf Moor zai cika.

Ings mai shekaru 22 ya ci kwallaye 11 a gasar Premier a Burnley wacce ta fice daga gasar bana, yayin da za ta koma buga Championship a badi.

Tshohon dan wasan Bournemouth ya na cikin tawagar kwallon kafar Ingila ta matasa 'yan kasa da shekaru 21 da za su fara gasar cin kofin nahiyar Turai a Jamhuriyar Czech.

Ings shi ne dan kwallo na biyu da Liverpool ta dauko, bayan da ta fara kulla yarjejeniya da James Milner na Manchester City a makon jiya.