West Ham na daf da daukar kociya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption West Ham United ta kare a mataki na 12 a kan teburin Premier bana

West Ham United na daf da daukar sabon koci da zai horar da kungiyar, bayan da ta tattuana da wadan da suka yi zawarcin aikin.

West Ham wacce ke buga gasar Premier tana neman kocin da zai maye gurbin Sam Allardyce wanda ya bar aikin a watan jiya, bayan shekaru hudu yana jagorancin kungiyar.

Cikin wadan da aka gana da su har da tsohon dan wasan West Ham Slaven Bilic wanda ya horar da Croatia a baya, inda ya sanar da cewa zai bar kocin Besiktas a watan jiya.

Shi ma tsohon kociyan Borussia Dortmund Jurgen Klopp ana alakanta shi da aikin da kuma mai horar da Real Sociedad.