Enrique zai ci gaba da horar da Barca

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A shekarar farko Enrique ya dauki kofuna uku a Barcelona

Kociyan Barcelona Luis Enrique zai ci gaba da jagorantar kungiyar, bayan da ya tsawaita kwantiragin shekara daya.

Kocin mai shekaru 45, ya dauki kofin La Liga da Copa del Rey da kuma kofin zakarun Turai a shekarar farko da ya fara aiki da Barcelona.

Shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu ne ya tabbatar da tsawaita kwantiragin Enrique a ranar Talata.

Enrique ya ki ya bayyana makomarsa a Barca, lokacin da ya dauki kofin zakatun Turai ranar Asabar bayan da suka doke Juventus da ci 3-1 a wasan karshe.

Tsohon dan kwallon Barca Enrigue wanda ya maye gurbin Tata Martino a bara, ya lashe kofuna uku a bana, wanda Pep Guardiola shi ma ya dauka a shekaru shida da ya yi.