Enyeama zai yi ritaya bayan kofin Afirka

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Enyeama shi ne dan wasan Nigeria na biyu da ya buga mata wasanni 100

Vincent Enyeama ya ce idan ya buga gasar cin kofin nahiyar Afirka a shekarar 2017 zai yi ritaya da buga wa tawagar kwallon kafar Super Eagles tamaula.

Mai tsaron ragar Nigeria mai shekaru 32, wanda yake murza leda a Lille ta Faransa, ya fara yi wa Super Eagles wasa a karawar da ta yi da Kenya a watan Mayun 2002.

Enyeama ya taka rawar gani a lokacin da Nigeria ta lashe kofin nahiyar Afirka a shekarar 2013 a Afirka ta kudu, yana kuma fatan sake yin hakan a shekarar 2017.

Golan ya ce yana fatan zai kafa tarihin da ba zai manta da shi ba a fagen kwallon kafa a Nigeria da Afirka da kuma duniya a gasar kofin Afirka na 2017.

Super Eagles za ta buga wasan neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka na shekarar 2017, a inda za ta kara da Chadi a karshen makonnan a Kaduna.

Nigeria tana rukunin da ya kunshi Masar da Chadi da kuma Tanzaniya.