Atletico za ta dauko Carlos Tevez

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tevez ya taimakawa Juve ta lashe kofin Serie A dana Kalubalen Italiya a bana

Kocin Atletico Madrid Diego Simeone ya ce wakilan kungiyar suna tattaunawa da Juventus domin su dauko Carlos Tevez.

Kocin ya shaida wa jaridun Spaniya cewa Tevez dan wasa ne da zai dace da murza leda a Atletico Madrid.

Tevez mai shekaru 31 ya nemi izinin daga Juventus cewar yana son barin kulob din a bana.

Simeone ya ce "Tevez ya kware wajen buga tamaula, kuma salon murza ledarsa za ta dace da yadda muke yin wasanninmu".

Kociyan ya kuma ce za su dauko Luciano Vietto daga Villarreal da kuma tsohon dan wasan Atletico Filipe Luis daga Chelsea.