BT zai nuna wasannin zakarun Turai

Image caption BT Sports zai nuna wasannin gasar cin kofin zakarun Turai a talabijin

Kamfanin BT sports zai nuna dukkannin wasanni 351 na gasar cin Kofin zakarun Turai da na Eurofa a gasar badi.

Kamfanin zai nuna wasu wasannin ga kowa da kowa, idan dai ka sayi kunshin yarjejeniyar kallon tashar talabijin ta BT Sports da ake kira Showcase.

Tashar ta talabijin dake tauraron dan Adam za ta nuna wasanni 12 na gasar cin Kofin Zakatun Turai da kuma wasanni 14 na wasannin Europa.

Gary Lineker da Jake Humphrey ne za su dunga gabatar da shirin, yayin da shi ma Rio Ferdinan zai dunga kasancewa a cikin shirin.