Manchester City tana yin fice - Hart

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption City ce ta kammala a mataki na biyu a kan teburin Premier bana

Mai tsaron ragar Manchester City Joe Hart ya ce City tana kara fadada a fagen tamaula a duniya a karkashin jagorancin shugabanta Khaldoon Al Mubarak.

Shugaban City, Khaldoon Al Mubarak, ya yi amanna cewa fitattun 'yan wasan kwallon kafa na kwadayin buga leda a kulob din ba domin albashi mai tsoka ba.

Hart ya ce "Al Mubarak shugaba ne na gari na kuma na amince da shi a matsayin wanda ke taka leda a kulob din".

Al Mubarak ya ce City tana da kayayyaki da tanade-tande da za ta iya daukar duk wani sanannen dan wasa a duniya, amma za ta fuskanci kalubale da zarar an bude kasuwar musayar 'yan kwallo ranar 1 ga watan Yuli.

Golan wanda ya tsawaita kwantiragi a City a Disambar bara, zai ci gaba da yin wasa a Ettihad har zuwa karshen kakar wasannin 2019.