Man City ta taya Sterling fan miliyan 25

Image caption Sterling yana shan matsi kan kokarin barin Anfield da yake son yi

Liverpool ta ki amincewa da tayin fan miliyan 25 da Manchester City ta yi kan a sayar mata da Raheem Sterling.

Liverpool ta kimanta darajar Sterling kan kudi fan miliyan 50 ga dan kwallon Ingila, wanda ake rade radin zai koma Arsenal ko Real Madrid da taka leda.

Dan wasan mai shekaru 20, ya koma Liverpool murza leda daga QPR a shekarar 2010 kan kwantiragin da zai kare a shekarar 2017.

Liverpool ta yi tayin za ta dunga bai wa dan kwallon fan 100,000 duk mako, yayin da ya ce ba maganar kudin da za a bashi bane.

A watan jiya koci Brendan Rodgers ya ce yana sa ran Sterling zai ci gaba da wasa a Anfield zuwa karshen lokacin da aka kulla yarjejeniya da dan wasan.