Sakamakon wasannin damben gargajiya

Image caption Alin Tarara daga Kudu da Bahagon Sisco daga Arewa babu kisa a damben

A ci gaba da wasannin damben gargajiya da ake yi a gidan damben Ali Zuma dake Dakwa a Abuja, an ci gaba da fafatawa ranar Alhamis.

An fara wasan farko ne tsakanin Shagon Inda daga Arewa da Garkuwan Shagon Mada daga Kudu na tsawon turmi uku, sai dai babu kisa a damben.

Dambe na biyu da aka taka Shagon Musan Kaduna ne daga Arewa ya kashe Shagon Audu na Mai Kashi daga Arewa a turmi na biyu.

An kuma sa zare tsakanin Bahagon Alin Tarara daga Arewa da Bahagon Sisco daga Kudu na tsawon turmi uku babu kisa alkalin wasa Ali Kwarin Ganuwa ya raba wasan.

Daga karshe a taka tsakanin Shagon dan Digiri daga Kudu da Shagon Musan Kaduna daga Arewa amma dare ya yi turmi daya suka yi babu kisa, za kuma aci gaba da wasannin ranar Juma'a.