Shekara daya rabon da a doke Ingila a kwallo

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rabon da a ci Ingila tun lokacin da Italiya ta lashe ta a gasar cin kofin duniya a Brazil a shekarar 2014

Wayne Rooney ya ce abin alfahari ne ace sun yi shekara daya ba a ci su a wasan tamaula tun bayan da suka kasa yin abin a zo a gani a gasar kofin duniya a Brazil.

Tawagar kwallon kafar Ingila karkashin jagorancin Roy Hodson ta lashe wasanni bakwai ta kuma yi canjaras a karawa biyu a cikin shekarar 2014-15.

Ingila za ta buga da Slovenia a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai ta badi, kuma shi ne wasan karshe da zai cika shekara daya tun bayan gasar cin kofin duniya.

Rabon da Ingila ta kafa irin wannan tarihin tun shekaru 24 da suka wuce, kuma Rooney ya ce ya kamata su lashe Sloveniya domin su kara samun martaba a fagen tamaula.

Ingila ce ke mataki na daya a rukuni na biyar a wasannin neman gurbin shiga gasar nahiyar Turai, kuma ta bai wa Slovenia wacce ke matsayi na biyu tazarar maki shida tsakani.

Karawar da Ingila za ta yi da Sloveniya a Ljubljana shi ne yake ciki shekara daya tun lokacin da Italiya ta doke ta a gasar cin kofin duniya da Brazil ta karbi bakunci a shekarar 2014.