Capello ya shiga tsaka mai wuya a Rasha

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rasha tana mataki na uku a kan teburi da sai ta buga wasan neman cike gurbi

Makomar Fabio Capello a matsayin kocin tawagar kwallon kafar Rasha na tangal-tangal, bayan da hukumar kwallon kasar za ta zauna taro.

Mai rikon kujerar kungiyar 'yan kwallon kafar Rasha Nikita Simonyan ya shaida wa wata kafar yada labarai cewar makomar Capello abar tambaya ce.

Simonya ya yi wannan jawabin ne sakamakon doke Rasha 1-0 da Austria ta yi a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Nahiyar Turai da suka yi ranar Lahadi.

Capello ya karbi aikin horar da Rasha a watan Yulin 2012 a inda ya kulla yarjejeniyar tsawaita zamansa tsawon shekaru hudu a Janairun 2014.

Rasha da Capello sun cimma matsaya ne domin kocin ya ci gaba da jagorantar kasar zuwa gasar cin kofin duniya da Rasha za ta karbi bakunci a shekarar 2018.