FIFA ta dakatar da 'yar wasan Nigeria, Njoku

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An hukunta Njoku ne bisa yi wa wata 'yar wasa dungu.

Kwamitin ladabtarwa na Fifa ya dakatar da 'yar wasan Najeriya, Ugo Njoku, daga buga wasanni uku a gasar cin kofin duniya na mata da ake yi a Canada.

Kwamitin ya dauki mataki kan Njoku ne saboda ta yi wa 'yar wasan Australia, Sam Kerr, dungu lokacin wasan da aka doke Super Falcons 2-0 ranar Juma'a.

Kwamitin ya bukaci 'yar wasan ta biya tarar $3,200, sannan ya gargade ta a kan yin muguwar halayya a lokacin wasa.

Hukuncin da aka yanke wa Njoku zai fara aiki ne nan take.