Chelsea na daf da daukar Falcao

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Monaco tana fatan ta sayar da Radamel Falcao ga kulob din dake sha'awar dan kwallon

Kulob din Chelsea na daf da kulla yarjejeniyar dauko Radamel Falcao na Manaco domin ya buga masa wasanni aro a badi.

Kungiyoyin biyu sun kusan cimma matsayar da za ta bai wa Falcao damar koma wa taka leda ga kulob din Chelsea zakarar kofin Premier bana.

Kwallaye hudu Falcao ya ci wa United a wasanni 29 da ya buga wasanni aro a kakar bana.

Falcao, mai shekaru 29, yana tare da tawagar kwallon kafar Colombia a inda suke fafatawa a gasar Copa America a Chile.