Swansea ta dauki Beattie mataimakin koci

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption James zai horar da 'yan wasa yadda ake zura kwallaye a raga

Kungiyar Swansea City ta dauki tsohon dan wasan Ingila James Beattie a matsayin mataimakin kociyanta.

Beattie, mai shekaru 37 ya buga kwallo tare da Garry Monk kociyan Swansea a kulob din Southampton.

Zai kuma yi aiki tare da Kristian O'Leary da Alan Curtis, bayan da aka dora masa nauyin koya wa 'yan wasan gaba yadda ake cin kwallaye a raga.

Beattie ya buga wa Southampton wasanni sama da 200, kuma ya buga wa tawagar kwallon kafar Ingila wasanni biyar.

Swansea ta kammala a mataki na takwas a kan teburin Premier bana da maki 56.