Dangote na shirin sayen Arsenal

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dangote ya fi shekaru 30 yana goyon bayan Arsenal

Mutumin da ya fi kowa arziki a Afrika, ya ce yana shirin sayen kungiyar Arsenal ta Ingila.

Attajirin dan Nigeria, Aliko Dangote ya ce idan ya kamalla gina matatar mansa zai samu damar mai da hankali wajen sayen kungiyar.

Dan shekaru 58, wanda arzikinsa ya kai fan biliyan 11 da rabi kuma ya ce tun a shekarun 1980 ya ke goyon bayan Gunners.

"Idan muka kamalla gina matatar mai, zan samu lokaci da kuma kudin da zai ba ni damar sayen kulob din," in ji Dangote a hirarsa da BBC Hausa.

BaAmurke Stan Kroenke ne ya fi kowa hannun jari a Arsenal sai kuma dan Rasha, Alisher Usmanov.

A baya Dangote ya nemi sayen Arsenal lokacin da Nina Bracewell-Smith ta saka na ta kason hannun jarin a kasuwa, kafin daga bisani ya janye a watan Afrilun 2011.

"A lokacin mutane da dama suna kokarin saya, kuma farashin ya yi tsada saboda mun yi yawa abin da ya sa muka janye kenan," in ji Dangote.