Premier: Chelsea za ta fara da Swansea

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea ce ta dauki Premier bana kuma karo na hudu a tarihi

Kungiyar Chelsea za ta fara buga gasar Premier ta badi da Swansea a filin wasanta na Stanford Bridge ranar 8-9 ga watan Agusta domin kare kambunta.

Manchester City -- wacce ta kammala gasar Premier ta bana a matsayi na biyu -- za ta ziyarci West Brom, yayin da Manchester United za ta karbi bakuncin Tottenham a Old Trafford.

West Ham za ta ziyarci Arsenal a Emirates, a inda Liverpool za ta bakunci Stoke City; sai wasan Newcastle da Southampton da kuma fafata wa tsakanin Leicester da Sunderland.

Sababbin kungiyoyin da suka hau Premier bana kuwa -- Bournmouth da Aston Villa -- Watford da Everton da kuma Norwich ta ke ce raini da Crystal Palace.