Liverpool ta ki sallama Sterling ga City

Image caption Manchester City na yunkurin dauko Sterling daga Liverpool

Manchester City ta kara kudin da ta fara taya Raheem Sterling zuwa fam miliyan 35, yayin da ake ganin Liverpool ba za ta sayar da shi ba.

Liverpool ta yi kiyasin cewa Sterling mai shekaru 20, wanda Arsenal da Real Madrid ke zawarci ya kai darajar kudi fan miliyan 50.

A makon jiya Liverpool ta ki amincewa da tayin fam miliyan 25 daga Manchester City.

Sterling ya koma Liverpool daga QPR a shekarar 2010, kuma sai a karshen kakar wasan 2017 kwantiraginsa za ta kare da kulob din.

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya ce yana fatan dan wasan zai ci gaba da buga tamaula a Anfield har zuwa lokacin da yarjejeniyar da ya kulla za ta kare.