Amurka ta ci Najeriya 1- 0

Hakkin mallakar hoto NFF
Image caption 'Yan kungiyar wasan kwallon kafa na Najeriya, Falconets

'Yan wasan kwallon kafa mata na kasar Amurka sun lallasa takwarorinsu na Najeriya da ci 1 da nema, a gasar cin kofin duniya na mata da ake gudanarwa a kasar Kanada.

An dai fafata tsakanin kasashen biyu ranar Larabar nan sai dai kuma Najeriya ba ta samu sa'a ba.

Ana dab da tafiya hutun rabin lokaci ne 'yar wasan Amurka, Wambatch ta samu nasarar daga ragar Najeriya. Kuma har aka kammala wasan Najeriya ba ta iya farkewa ba.

Wannan nasara ta ba wa Amurka kasancewa zakara a rukunin (D) sannan za ta zamo daya daga cikin ajin kasashe 16 da za su taka leda, a Edmonton ranar Litinin.