Uche zai koma tamaula a Mexico

Image caption Uche ya zama dan kwallon farko da ya koma Mexico daga Afrika

Dan kwallon Nigeria, Ikechukwu Uche ya ce a shirye yake ya fuskanci sabon kalubale a yayinda zai koma taka leda a kasar Mexico.

Kungiyar Tigres de la UANL ta Mexico ta sayi tsohon dan wasan Villareal mai shekaru 31, inda ta kulla yarjejeniyar shekaru uku tare da shi.

Uche ya zama dan kwallon Afrika na farko da ya koma taka leda a kungiyar wacce ta lashe gasar Mexico sai uku a baya.

"Wannan sabon kalubale ne kuma ina son in gwada," in ji Uche.

Uche ya koma Villareal ne a shekarar 2011 daga Real Zaragoza bayan da ya taka leda a kungiyoyin Recreativo Huelva da kuma Getafe duk a kasar Spain.

Ya zura kwallaye 103 cikin shekaru 13 a gasar La Liga.