Kakuta ya koma Sevilla

Image caption Kakuta ya shafe shekaru shida tare da Chelsea

Dan kwallon Cheslea, Gael Kakuta ya koma kungiyar Sevilla ta Spain.

Kakuta mai shekaru 23, ya koma Stamford Bridge daga Lens a shekara ta 2007 amma ya shafe kakar wasan da ta wuce a matsayin aro a Rayo Vallecano.

Dan kwallon Faransa din ya buga wa Chelsea wasanni sau 16 sannan ya tafi aro a kungiyoyi daban-daban shida.

A shekara ta 2009, Chelsea ta shiga cece-kuce game da sayen Kakuta daga Lens inda sai da aka shiga gaban kuliya kan batun.