Ban taba shan kwaya ba - Farah

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Farah ya lashe zinare biyu a gasar Olympics

Dan tseren Biritaniya Mo Farah ya ce bai taba shan kwaya mai kara kuzari da aka haramta ba a rayuwarsa.

Ya bayyana haka ne bayan da ake zargin kocinsa, Alberto Salazar da bai wa dan tseren Amurka Galen Rupp kwaya mai kara kuzari da aka haramta.

Zakaran wasan Olympics din, Farah ya ce Salazar ya tabbatar masa cewa an yi masa sharri kuma gaskiya za ta yi halinta.

"Ban taba shan haramtattun kwayoyi ba, masu kara kuzari ba a rayuwata," in ji Farah.

Darijar Daily Mail ta ce, sau biyu Farah ya kuskure ba a yi masa gwajin shan kwaya mai kara kuzari kafin ya samu lambar zinare a tseren mita 5,000 da kuma 10,000 a gasar Olympics ta 2012.