Kano Pillars ta doke Giwa FC da ci 4-1

Hakkin mallakar hoto kanopillarsweb
Image caption Kano Pillars ce ke rike da kofin Premier bara da ta lashe

Kano Pillars ta samu nasara a kan Giwa FC da ci 4-1 a gasar Premier Nigeria wasannin mako na 12 da suka kara ranar Alhamis.

Pillars ta ci kwallayen ne ta hannun Rabi'u Ali wanda ya ci biyu daga bugun fenariti, sannan Adamu Mohammed shi ma ya zura kwallaye biyu a raga a wasan.

Giwa FC ta zare kwallo daya ta hannun Ocheme Edoh saura minti takwas a je hutun rabin lokaci.

Sauran sakamakon wasanni biyu da aka buga FC Taraba rashin nasara ta yi a hannun Wikki Tourist har gida da ci 2-1, sai Sunshine Stars da ta doke Warri Wolves da ci 2-1.

Da wannan sakamakon Sunshine Stars ta dare mataki na daya a kan teburi da maki 23, yayin da Enyimba ke biye da maki 22, sai Kano Pillars da maki 21 a mataki na uku.