Southampton ta dauki Cedric Soares

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasa na biyu da Southampton ta dauko a bana

Southampton ta dauki mai tsaron bayan Portugal, Cedric Soares, kan yarjejeniyar shekaru hudu daga kulob din Sporting Lisbon.

Mai shekaru 23, shi ne dan kwallo na biyu da kulob din ya dauka, bayan da ya fara sayo Juanmi daga Malaga.

Soares ya fara buga wa tawagar kwallon kafar Portugal tamaula a watan Oktoban 2014, ya kuma yi mata wasanni hudu.

Southampton za ta buga wasan neman gurbin shiga gasar Europa, bayan da ta samu matsayin hakan sakamakon kammala Premier bana a mataki na bakwai da ta yi.